A ranar Juma’a 5 ga watan Disamba 2025, ne aka raba jadawalin ƙasashen da za su fafata a gasar cin kofin ƙwallon ƙafar duniya FIFA WORLD CUP, 2026 wadda za’ayi a kasashen Amurka, Mexico, da Kanada.
Bikin raba jaddawalin ya gudana ne a birnin Washington na ƙasar Amurka.

Heidi Klum da Kevin Hart tare da Danny Ramirez suka jagoranci bikin.

Lokacin bikin FIFA ta karrma shugaban ƙasar Amurka Donald Trump da lambar yabo na Zaman lafiya.
Ƙasashe 48, da suka fito daga nahiya daban-daban dake fadin duniya ne zasu fafata a tsakaninsu ga yadda jadawalin ya kasance bisa jerin rukuni 12.
- Rukunin A:
- Mexico
- Afirka ta Kudu
- Koriya ta Kudu
- Duk Ƙasar da ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin D
- Rukunin B:
- Canada
- Qatar
- Switzerland
- Duk Ƙasar da ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin A
- Rukunin C:
- Brazil
- Moroko
- Scotland
- Haiti
- Rukunin D:
- Amurka
- Paraguay
- Australia
- Duk Ƙasar da ta fito a wasan cike gurbi na
- Uefa rukunin C
- Rukunin E:
- Germany
- Ivory Coast
- Ecuador
- Curacao
- Rukunin F:
- Netherlands
- Japan
- Tunisia
- Duk Ƙasar da ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin B
- Rukunin G:
- Belgium
- Egypt
- Iran
- New Zealand
- Rukunin H:
- Spain
- Saudi Arabia
- Uruguay
- Cape Verde
- Rukunin I:
- France
- Senegal
- Norway
- Duk Ƙasar da ta fito a wasan cike gurbi na Fifa rukunin 2
- Rukunin J:
- Argentina
- Algeria
- Austria
- Jordan
- Rukunin K:
- Portugal
- Uzbekistan
- Colombia
- Duk Ƙasar da ta fito a wasan cike gurbi na Fifa rukunin 1
- Rukunin L:
- England
- Croatia
- Panama
- Ghana
Inda mai masaukin baki ƙasar Mexico zasu bude gasar tsakanisu da ƙasar Afirka ta Kudu, ranar 11 ga watan Yuni 2026, a Azteca Stadium – iconic.
Sauran Ƙasashen suke neman shigowa cikin gasar, wadda sai sun buga wasan cike gurbi su be kamar haka.
Italiya, Wales, Bosnia-Herzegovina, Arewacin Ireland
Ukraine, Poland, Albaniya, Sweden
Turkiyya, Slovakiya, Kosovo, Romaniya
Denmark, Czech Republic, Republic of Ireland, North Macedonia
DR Congo, Jamaica, New Caledonia
Iraqi, Bolivia, Suriname


