Fiye da fararen hula 1000 suka rasa rayukan a lokacin da kungiyoyin dakaru ‘yan sa kai suka karbe ikon wani sansanin ‘yan gudun hijira da yunwa ta yiwa katutu a yankin Darfur na kasar Sudan, a watan Aprilu, wannan ya hada da kaso uku daga cikin su, wadanda aka yiwa kisan gilla, a cewar wani rahoto daga ofishin hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya.
Watanni, kafin kai hare-haren na 11 zuwa 13 ga watan Afrilu, dakarun sa kan na Rapid Support RSF sun hana shiga da abinci da sauran abubuwan bukatu a sansanin Zamzam da ke yammacin Dafur, wanda ya ke dauke da mutane kusan miliyan 1, da suka rasa matsuguni sakamakon yakin basasa, a cewar rahoton na Majalisar Dinkin Duniya.
Majisar Dinkin Duniya ta ce, dakarun na RSF, sun afkawa farar hula ta hanyar kashewa, wahalarwa, sacewa da kuma cin zarafi, kuma an yiwa a kalla mutane 319 kisan gilla yayin da suke kokarin tserewa


