Wata gobara ta tashi a ɗaya daga cikin ofisoshin hukumar karɓar harajin cikin Gida ta tarayya (FIRS) da ke Abuja Najeriya a ranar Asabar.
Wani bidiyoyi da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna wutar tana ƙone wasu sassan ginin, lamarin da ya jawo firgici a yankin.
A cikin wata sanarwa da Sikiru Akinola, jami’i a fannin yada labrai na hukumar FIRS ya sanya wa hannu, hukumar ta ce gobarar ta tashi ne a ofishinta da ke Lamba 15, titin Sokode Crescent, Wuse Zone 5.
“Gobarar, wadda ta tashi a bene na huɗu na ginin, jami’an tsaronmu da ke bakin aiki sun ɗauki mataki cikin gaggawa,” in ji sanarwar.
“Da saurin tallafin hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya da sauran jami’an agajin gaggawa, an samu nasarar shawo kan wutar tare da hana ta yaɗuwa zuwa wasu sassa.”


