Ƙasar Guinea kuma an zabi Mamady Doumbuya, madugun sojojin da suka yi juyin mulki a zaman shugaban kasa, kamar yadda kwarya-kwaryar sakamakon zabe da aka bayyana jiya talata, mataki da ya kammala shirin maido da kasar kan turbar demokuradiyya, ga kasar dake Afirka ta yamma da Allah Ya yiwa albarkar karfe.
Tsohon kwamandan dakaru na musamman, wanda ake kiyasin dan shekaru 40 ne da haifuwa, Dumbouya ya yiwa shugaba Alpha Conde wanda yake shugabancin kasar tun 2010 juyin mulki shekara ta 2021. Juyin mulkin na kwango yana daga cikin jerin sauye sauye gwamnati da bakin bindiga har tara a kasashe da suke yammaci da kuma wadanda suke yankin tsakiyar Afirka daga shekara ta 2020.
Kwarya-kwaryar sakamakon zaben da aka bayar a talata, ya nuna shugaba Doumbuya ya sami kashi 86.7 cikin dari na kuriu da aka kada, a zaben da aka yi ranar 28 ga watan Disemban 2025, rinjaye mai karfi da zata hana shi zuwa zagaye na biyu a zaben,
Tuni dai ake sa ran shugaba Doumbuya ya sami nasara a zaben, domin tsohon shugaban kasa Alpha Conde, da dadadden shugaban ‘yan hamayya Cellou Dalein Diallo suke gudun hijira, wadda ya baiwa shugaba Doumbuya damar fuskantar tsirarun ‘yan hamayya da suka kasa hada kai su takwas.
Kotun kolin kasar tana da kwanaki takwas ta tabbatar da sakamakon zaben, idan har akwai wadanda suke jayayya kan wannnan sakamako.


