Gwamnatin Kano ta umarci jami’an tsaro su dakatar da masu yunkurin kafa hukumar Hisbah mai zaman kanta.
Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da umarnin zantaswa da ya haramta wata kungiya da ke aiki da sunan “Independent Hisbah Fisabilillahi” Wannan umarni da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu, mai dauke da ranar 8 ga Disamba, 2025, ya bayyana cewa gwamnati ta gano cewa ana ci gaba da daukar ma’aikata, horaswa da tura matasa cikin kungiyar ba tare da wata doka ko izini ba, kana kuma cikin sabawa dokar Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.
Yayin da yake mika sakon ga manema labarai, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa Hukumar Hisbah ce kadai hukuma ta doka da ke da ikon jagorantar dukkan ayyukan Hisbah a fadin jihar.

Gwamnati ta ce bullar wannan kungiya ta daban wani yunkuri ne na kafa wata hukuma ba bisa ka’ida ba, lamarin da zai iya haifar da tashin hankali da kuma take matsayin hukumar Hisbah ta jihar.
Gwamnan ya kuma bayyana dukkan ayyukan kungiyar a matsayin “haramtattu, ba bisa doka ba kuma babu inganci,” yana gargadin cewa duk wani kaya da ya yi kamanceceniya da alamomi ko ikon Hukumar Hisbah zai fuskanci hukunci.
Gwamna Yusuf ya umarci Rundunar ‘Yansanda ta Najeriya, Hukumar DSS, NSCDC da sauran hukumomin tsaro da su binciki wadanda ke goyon bayan kungiyar, su dakatar da duk wani ci gaba da ake yi na daukar ma’aikata ko horaswa, sannan su dauki matakan da suka dace don hana tabarbarewar tsaro a jihar Kano.


