Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnan Neja Bago Na Cin Zarafin Talakawan Da Suka Zabe Shi
Published: November 18, 2025 at 9:41 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

Wata haɗakar kungiyoyin fararen hula a Najeriya ta nemi gwamnatin Amurka da ta kakabawa Gwamna Umar Mohammed Bago na Jihar Neja takunkumin hana shiga ƙasar, wato ta hana shi bisa tare kwace duk wasu kaddarori na Gwamnan dake kasar ta Amurka.
Kungiyar dai ta zargi Gwamna Umar Bago da yin karan tsaye ga hakkin Dan Adam sannan da keta duk wasu hakkoki na Demokuradiyya,
A cikin wata takardar koke da suka aikawa Sakataren Harkokin Wajen Amurka ta hannun Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, ƙungiyar mai suna (Concerned Citizens and Defenders of Democracy in Nigeria) ta ce gwamnan yana amfani da karfin mulki wurin kuntatawa masu sukar salon Mulkinshi duk da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da  ta’azzara a jihar.
Kwamred Yusuf Sitizin jigo a cikin wannan kungiya kuma wakilin Kungiyar Amanasti International yayi karin haske akan dalilinsu na daukar wannan mataki.
To Sai dai tini Gwamnatin Jihar Nejan tayi watsi da wadannan zarge zarge na wannan kungiya tare da nesanta Gwamna Bago daga duk wani zargi na cin zarafin Dan Adam Alh. Abdulbakee Ebbo shine Mataimaki na musamman ga Gwamna Umar Bago akan Kafofin sadarwa na zamani, yayi magana a madadin Gwamnatin Jihar ta Neja ga abinda yake cewa.
https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2025/11/Karar-Gwamnan-Jihar-Neja-Gwamna-Umar-Bago.mp3
Labarai

Post navigation

Previous Post: Shirin Dare 2030 UTC Yau Talata 11.18.2025
Next Post: Addini Ko Kabilanci Basu Da Gurbi Cikin Ta’addanci

Karin Labarai Masu Alaka

Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika
Jami’an Diflomasiyyar Iran Dana Amurka Sun Tattauna A Kasar Oman Afrika
Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi Labarai
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha: Tura Sojojin Birtaniya Ukraine Zai Kara Ta’azzara Yaki Labarai
Jaura Ta Bayyana A Wasu Jihohin Amurka Labarai
Jakadan Amurka A Poland Ya Yanke Hulda Da Kakakin Majalisar Kasar Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Rahoton MDD Yace An Kashe Fiye Da Farar 1000 A Sudan Labarai
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ga Alamu Jakuna Za Su Bace A Doron Kasa Nan Da Shekaru 5 Labarai
  • Sojojin Kasar Uganda Sun Bazama Neman Bobi Wine Sakamakon Rikicin Bayan Zabe Siyasa
  • Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Najeriya Ta Tabbatar Da Kyautata Rayuwar Mambobin ta Labarai
  • Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai
  • An Kama Wani Da Abubuwan Fashewa A Zamfara Najeriya
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Litinin 11.17.2025 Rediyo
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.