Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya a ranar Talata, ya karɓi baƙuncin takwaransa na Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, tare da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Siyasa da Sauran Al’amura, Hon. Ibrahim Kabir Masari, don ƙaddamar da muhimman ayyuka da aza tubalin gina Sakatariyar Gundumomin Ci Gaba (LCDAs) a jihar.

Sanarwar Daraktan harkokin yada labaran gwamnatin jihar Gombe sun bayyana cewa, ayyukan da Gwamna Mai Mala Buni ya ƙaddamar, waɗanda suka haɗa da Sabuwar Sakatariyar Karamar Hukumar Nafada, da Gadar Nafaɗa mai gaɓa (4-Span), da Makarantar Tsangaya wassu manyan ayyuka ne da gwamnatin Inuwa Yahaya ta aiwatar, waɗanda suka yi tasiri mai yawa ga harkokin zamantakewa, tattalin arziƙi da shugabanci a Ƙaramar Hukumar Nafaɗa da kuma al’ummomin dake kewaye da ita.
Kafin gina sabuwar Sakatariyar, ma’aikatan Ƙaramar Hukumar suna aiki ne cikin wani mummunan yanayi wanda ba shi da tasiri wajen gudanar da gwamnati a zamanance.
Gadar ta Nafaɗa mai gaɓa 4, ta magance manyan ƙalubalen da mutanen yankin suka daɗe suna fuskanta. Kafin a gina gadar, hanyar bata biyuwa musamman a lokacin damina.
Ita kuma babbar Makarantar Tsangaya dake Nafada an tsara ta ne don samarwa Almajirai yanayi mai tsari da tallafin a harkokin karatunsu.
Wani aikin kuma wanda babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin siyasa da sauran su Hon. Ibrahim Kabir Masari ya ƙaddamar, shi ne hanyar Kwanan Rugaji zuwa Almakashi mai tsawon kilomita 7 da rabi tare da ratse zuwa Galgaldu wacce ta haɗe Ƙaramar Hukumar Funakaye ta jihar Gombe da wassu garuruwa na Jihar Yobe.
Hanyar, wacce tsawon shekaru al’ummomin yankin ke fama cikin mawuyacin hali musamman a lokacin damina, yanzu ta buɗe tare da ƙarfafa harkokin tattalin arziki a faɗin yankin.
Mai taimakawa Shugaban Ƙasan ya kuma ƙaddamar da wani katafaren rukunin shaguna 66 a Bajoga, wanda aka sanyawa sunan marigayi Sarki Muhammadu Kwairanga don girmamawa.

An tsara wannar cibiyar kasuwanci ce don haɓaka ayyukan kasuwanci, ƙarfafa ci gaban tattalin arziƙin yankin da kuma samar da yanayi mai kyau na kasuwanci ga ‘yan kasuwa.
A wajen bikin aza harsashin ginin sakatariyar gundumar ci gaba ta Ƙaramar Hukumar Funakaye ta kudu a Tongo da kuma sakatariyar gundumar ci gaba ta Nafada ta Kudu a Birin Fulani, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa ci gaban ya biyo bayan kirkirar gundumomin ci gaba 13 ne da gwamnatinsa ta yi, wani mataki da aka tsara da nufin samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma kawo gwamnati kusa da jama’a.
Yace “Yau wata muhimmiyar rana ce a ci gaba da kokarinmu na zurfafa demokraɗiyya da kuma zaburar da harkokin ci gaba daga tushe. Gina harsashin sakatariyar gundumar ci gaba ta Funakaye ta Kudu a Tongo da na Nafada ta kudu a Birin Fulani sakamako ne kai tsaye na shawarar gwamnatinmu na ƙirƙirar yankunan ci gaban ƙananan hukumomi 13”.
“An tsara waɗannan gundumomin ci gaban ne don samar da ci gaba mai ma’ana da kuma tabbatar da cewa gwamnati ta kusanci al’ummarmu. Hangen nesanmu a bayyane yake: nan gaba kadan waɗannan gundumomin ci gaba, za su rikiɗe su zama cikakkun ƙananan hukumomi yayin da muke ci gaba da ƙarfafasu,” in ji shi.

Yace za a gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi nan gaba a jihar tare da gundumomin ci gaban don ƙarfafa halaccinsu da kuma ƙarfafa demokraɗiyya daga tushen.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yaba da rawar da gundumomin ci gaban ke takawa wajen hamzarta ci gaban jama’a, inda ya bayyana cewa Jihar Gombe ta samu kwarin gwiwa daga gagarumin nasarar da Jihar Legas da sauran jihohin ƙasar nan suka samu sanadiyar ƙirƙiro gundumomin na ci gaba.
Ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesa da jajircewarsa wajen ƙirƙiro gundumomin na ci gaba a lokacin da yake Gwamnan Jihar Legas.
“Mun samu kwarin gwiwa daga tasirin da wannan tsari ya yi a Jihar Legas da sauran jihohi. Dole ne in yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda hangen nesa da jajircewarsa wajen samar da gundumomin ci gaba a lokacin da yake Gwamnan Jihar Legas. Wannan hangen nesa ya ci gaba da haifar da riba mai yawa, kuma muna da yaƙinin cewa Jihar Gombe za ta samu gagarumar nasara a wannan tsari”, in ji shi.
Gwamnan ya jaddada cewa kamar gwamnatocin ƙananan hukumomi da ake da su, sabbin gundumomin ci gaban da aka ƙirƙiro za su fi maida hankali ne a fannoni guda hudu waɗanda suka haɗa da tsaro, kiwon lafiya matakin farko, ilimi da noma, waɗanda gwamnan yace su ne ginshikin kawo sauyi da ci gaba ga jama’a musamman na yankunan karkara.
A jawabinsa a lokacin bukukuwan, Gwamna Mai Mala Buni ya yabawa takwaransa na Gombe kan abin da ya bayyana a matsayin shirye-shirye masu muhimmanci da za su ƙarfafa shugabancin ƙananan hukumomi.
Ya yaba da yadda ci gaban jihar ke tafiya cikin tsanaki, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai da haɗin gwiwa tsakanin gwamnonin Arewa wajen magance ƙalubalen da ake fuskanta, musamman a fannonin tsaro da ci gaba.
Ya yi ƙira ga al’ummomin da aka aiwatarwa ayyukan da duk al’ummar jihar Gombe su ci gaba da goyon bayan Gwamna Inuwa Yahaya a kokarinsa na kawo sauyi a jihar, yana mai kiran a ƙara addu’o’in neman ɗorewar zaman lafiya da ci gaba a faɗin jihar Gombe, Arewa da kuma ƙasa baki ɗaya.
Da yake jawabi a lokacin da aka ƙaddamar da hanyar Kwanar Rugaji zuwa Almakashi mai tsawon kilomita 7 da rabi, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Siyasa da Sauran Al’amura, Hon. Ibrahim Kabir Masari, ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya da Gwamnatin jihar Gombe kan saita tsarin ci gabanta da Ƙudurin Sabunta Fata na Gwamnatin Tarayya, inda ya bayyana aikin a matsayin wanda ke nuna shugabanci mai ma’ana da kuma ririta dukiyar jama’a yadda ya kamata.
Tun da farko da yake jawabi, Darakta Janar na Hukumar Haɗin Gwiwar Ci Gaba ta jihar Gombe, Builder Mahmood Yusuf, ya bada cikakken bayani game da ayyukan da ake gudanarwa na haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi, yana mai yabawa da ingancin ayyukan da kuma kammalasu a kan lokaci.

A yayin ziyarar tasa a ƙananan hukumomin Funakaye da Nafada, Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranci baƙi da tawagarsa zuwa gaisuwar ban girma ga Sarakunan Funakaye da Nafada. Sarakunan biyu sun godewa Gwamnan bisa ziyarar, da kuma gagarumin aikin da gwamnatinsa ta yi don ci gaban yankunansu, inda suka tabbatar masa da ci gaba da goyon baya da biyayyarsu ga ci gaban jihar Gombe.
A Masarautar Funakaye, Mai Martaba, Alhaji Yakubu Muhammad Kwairanga, ya karrama bakin gwamnan ta hanyar ba su sarautun gargajiya.
Yayinda aka naɗa Gwamna Mai Mala Buni a sarautar ‘Dikuman Funakaye’ shi kuwa Ibrahim Masari an naɗa shi ne a sarautar ‘Dan Saran Funakaye’.
Hakazalika shima Sarkin Nafaɗa, Alhaji Muhammadu Dadum Hamza ya baiwa Gwamna Buni da Hon. Masari sarautu bi da bi.


