Masana da manazarta a fannin tattalin arziki a Najeriya sun fara fashin baki akan kasafin kudi da Gwamnatin jihar Kano ta shirya domin tunkarar shekarar kudi ta badi.
A jiya Laraba ne dai gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin a zauren majalisar dokokin, inda yace gwamnatin jihar ta shirya kashe kusan naira triliyon guda da rabi a shekarar kudi ta 2026 dake tafe.
Yace bangaren ilimin shine ya samu kaso mafi tsoka da kashi 30 cikin dari, yayin da aka kebewa fannin ayyukan raya kasa kashi 68 na gundari kasafin, inda gwamnati zata maida hankali akan kammala ayyaka da ake gudanarwa tare da kirkiro wasu sabbi.

Sai dai masanin tattalin arziki, Dr. Abdussalam Kani, yace alkaluman dake cikin kasafin sun ci karo da alkaluman da aka fitar a yayin taro na masu ruwa da tsaki, da kwararru kan tattalin arziki da Jami’an gwamnatin Kano da akayi a kwanakin baya, game da hasashen abin da gwamnatin ka iya samu na kudaden shiga a badi.
Yace yanzu kalubale ne akan majalisar dokokin ta Kano ta dai-daita alkaluman kasafin na kusan Naira tiriliyon guda da rabi, domin kuwa sun zarce alkaluman da ke cikin takardar M-TEF, wadda aka mikawa majalisar dokokin gabanin gwamnan ya gabatar da kasafin.
Dr Abdussalam Kani yace takardar M-TEF, mai dauke da hasashen da masana da Jami’an gwamnati game da kudaden shiga na gwamnati a shekara ta 2026 wadda bai wuce naira biliyan dari takwas ba, kuma doka tace tilas ne kasafin da gwamna ya shirya yayi dai-dai da hasashen masana cikin takardar M-TEF.

A nasa bangaren, comrade Salisu Gambo, gudana cikin ‘yan gwagwarmayar shugabanci na gari a Najeriya, yace kamata yayi ace banaren tsaro na biye da na ilimi wajen samun kaso mafi tsoka a cikin kasafi, a don haka akwai bukatar majalisar dokokin ta sake nazarin kason da aka kebewa al’amuran tsaro a jihar.
A nan gaba ne, ake sa ran majalisar dokokin zata kira taron jin ra’ayin jama’a, domin karbar kasidu da shawarwari daga kungiyoyi da dedekun mutane kan yadda suke ganin za’a inganta kasafin domin ya dace da muhimman bukatun al’umar jihar ta Kano su fiye da miliyan 20.


