Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa rundunar kar-ta-kwana domin ƙarfafa tsaro a tashoshin mota da sauran muhimman wuraren taruwar jama’a a faɗin jihar.
Wannan na cikin sanarwar da Daraktan Yada Labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi 14 ga Disamba 2025.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne domin dakile shigowar masu aikata laifuka, musamman a wuraren da ake yawan zirga-zirga, ciki har da tashoshin mota da wuraren shigowa da fita daga birnin Kano.
Rundunar kar-ta-kwanan za ta riƙa sa ido, tattara bayanan sirri da aiwatar da ayyukan tsaro tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sanarwar ta ƙara da cewa aikin rundunar zai shafi har da gidajen mai da sauran wuraren taruwar jama’a da ake ganin zai iya haifar da barazanar tsaro.


