Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta miƙa motocin yaki masu sulke guda 13 ga Gwamnatin Jihar Kebbi, domin ƙarfafa yaƙi da ’yan bindiga da sauran laifuka a jihar.
An miƙa motocin ne a Gidan Gwamnati da ke Birnin Kebbi, inda Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, CP Bello Sani, ya ce an turo su ne daga hedikwatar rundunar a Abuja bisa umarnin Babban Sufeton ’Yan Sanda.
A martaninsa, Gwamna Nasir Idris ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugabancin rundunar ’yan sanda, yana mai cewa motocin za a tura su zuwa muhimman wuraren da ke fama da matsalolin tsaro, musamman a kan iyakokin Zamfara da Neja, domin bai wa manoma damar yin girbi cikin aminci.
Gwamnan ya jaddada cewa, tsaro ne ginshiƙin ci gaba, tare da tabbatar da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro cikakken goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kebbi.


