Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bukaci daukacin ‘yan Najeriya dake zaune a kasar Iran da sauran kasashen yankin tekun fasha (Gulf) da su kasance cikin tsananin sa ido da kiyaye kai, biyo bayan takun-saka da hare-haren soji da suka barke a yankin.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar a ranar Asabar, 28 ga Fabrairu, 2026, wadda kakakin ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, gwamnatin ta bayyana cewa tana sanya idanu sosai kan yadda al’amura ke sauyawa bayan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan wasu wurare a Iran, da kuma martanin da ita ma Iran din ta mayar.
Don tabbatar da tsira da lafiyar ‘yan kasa, ma’aikatar ta fitar da wasu shawarwari guda biyar (5) kamar haka:-
* Gwamnati ta shawarci ‘yan Najeriya da su guji zirga-zirga a kusa da sansanonin soji, gine-ginen gwamnati, ko wuraren da ake ganin za su iya zama matattarar rikici.
* An bukaci mutane da su zauna a gida muddin ba wata muhimmiyar bukata ce ta fitar da su ba, sannan su guji shiga taron jama’a ko zanga-zanga.
* An bukaci ‘yan kasa da su kiyaye dukkan dokoki da matakan tsaro da hukumomin kasashen da suke ciki suka gindaya.
* Ma’aikatar ta bukaci mutane da su rinka sauraron kafafen yada labarai na kasa da kasa masu gaskiya, sannan su kiyayi yada labaran bogi.
* Sanarwar ta tabbatar da cewa ofisoshin jakadancin Najeriya da ke Tehran (Iran), Qatar, Bahrain, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), da Saudi Arabiya suna cikin shirin ko-ta-kwana don tallafa wa duk wani dan Najeriya da ya shiga cikin matsala.
A karshe, Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga daukacin bangarorin da rikicin ya shafa da su kwantar da hankalinsu, su ajiye makamai su koma kan teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya a duniya.
Ta kuma sake jaddada cewa kare rayukan ‘yan Najeriya a duk inda suke a fadin duniya shi ne babban burin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.


