Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bukaci cikakken hadin kai da jarumta domin shawo kan matsalolin tsaro da na tattalin arziki da ke kara ta’azzara a Arewacin Najeriya.
Da yake jawabi a taron hadin gwiwar Kungiyar Gwamnonin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa a Kaduna, Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada bukatar daukar matakan da suka dace domin kare makomar yankin.
Ya nuna damuwa kan karuwar sace-sacen jama’a a jihohin Kebbi, Kwara, Kogi, Kano, Niger da Sokoto, da kuma sake tashin rikicin Boko Haram a Borno da Yobe, yana mai cewa wadannan hare-hare sun zamo babbar barazana ga zaman lafiya da wanzuwar cigaba.

Gwamnan ya jajanta wa iyalai da abin ya rutsa da su da gwamnatocin jihohin da abin ya shafa, tare da yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan gaggawar kubutar da wasu daga cikin daliban da aka sace.
Ya kuma tabbatar da goyon bayan kungiyar ga ci gaba da kokarin ceto sauran wadanda ke hannun masu garkuwa da mutane.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi gargaɗi kan jefa siyasa ko addini da kabilanci a cikin matsalar tsaro, yana mai cewa wannan rikici ya shafi kowa ba tare da bambanci ba.
Kan an danganta tsanantar matsalolin tsaro da talauci, jahilci, sauyin yanayi da rashin ingantattun ababen more rayuwa, yana mai cewa zaman lafiya ba zai tabbata ba sai an zuba jari a bangaren ci gaban dan Adam da tattalin arziki.
Daya daga cikin mahimman batutuwan taron shi ne yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewacin kasar.
Ya bukaci shugabannin Arewa su dauki matakin gaggawa da na hadin kai don magance matsalar.
Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada matsayar Arewa na goyon bayan kafa ‘yan sandan jihohi domin magance ta’azzarar tsaro a yankin.
Ya yaba wa shugaban kasa kan umarnin da ya bai wa Majalisar Dattawa da ta Wakilai da su hanzarta gyaran kundin tsarin mulki domin aiwatar da wannan manufar.

Ya kara jaddada cewa samun dorewar zaman lafiya ya dogara ne kan hadin gwiwar kowane sashi na al’umma sarakunan gargajiya a matsayin masu sulhu, malaman addini a matsayin masu yada zaman lafiya, shugabannin siyasa a matsayin masu gina ci gaba ba rarrabuwa ba. Hukumomin tsaro masu aiki cikin hikima, alkalan kotuna masu hanzarta hukunci da kuma al’umma a matsayin abokan hadin gwiwa wajen tsaron yankuna.
Tun Farko, a jawabinsa na maraba, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce Arewa na fuskantar babban kalubale na tsaro, tattalin arziki da zamantakewa wanda ke bukatar hadin kai da sabbin dabaru.
Ya jinjinawa takwarorin sa kan ci gaba da karfafa tattaunawa da aiki tare, yana mai cewa hakan ne kadai hanyar samun dorewar zaman lafiya da ci gaba a yankin.
Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yaba wa kungiyar karkashin jagorancin Gwamna Inuwa Yahaya kan himmar da ta ke nuna wa wajen shawo kan manyan matsalolin da ke addabar Arewa.
Ya ce sarakunan gargajiya da malaman addini na goyon bayan wannan kokari, musamman tattaunawa da aka dade ana yi domin magance matsalolin tsaro, karfafa hadin kai da inganta walwalar al’umma.
Ya bukaci gwamnonin Arewa da su ci gaba da zama tsintsiya madaurin ki daya wajen samar da ingantattun hanyoyin dawo da kwanciyar hankali da ci gaba a yankin.


