Kakakin kungiyar ‘yan tawaye ta M23 da ke gwabza fada da rundunar sojin jamhuriyar Demokradiyar Congo, Willy Ngoma ya rasa ran sa biyo bayan wani hari daga jirgin sama mara matuki na drone a gabashin Congo a ranar Talata, a cewar wasu manyan jami’an kungiyar su biyu.
Harin ya auku ne kusa da garin Rubaya dake arewacin Kivu, da wajajen karfe 3 na tsakar dare, kuma ya biyo bayan hare-hare da aka sha kaiwa na drone a yankin, wanda rundunar sojan Congo ke da alhakin su, a cewar Jami’an M23 da suka zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Rubaya wuri ne na musamman da ake hako ma’adanin coltan, kuma yana samar da kashi 15 cikin 100 na coltan din da ake samu a duniya, saboda haka ya zamo wata mattatara ta tattalin arziki ga ‘yan tawayen na M23.


