Ƴansanda Sun Musanta Zargin Kashe Ɗan Achaba a Gombe
Rundunar ƴansandan jahar Gombe a Najeriya ta ce babu wanda jami’an ta suka kàshe kamar yadda ake yaɗawa a kafafan sada zumunta da safiyar Laraba.
Kakakin rundunar ƴansandan jhar, DSP Buhari Abdullahi, yace ɗan Achaban da ake zargi wani ɗansanda ya kashe sunansa Haruna Muhammad kuma tuni aka yi masa jinyar raunin da ya ji sakamakon faɗuwa da ya yi a mashin lokacin da ƴansanda suka yi ƙoƙarin kamashi saboda ya ɗau mutum 2 a Babur.
Shima shugaban ƙungiyar ƴan Achaba ta jahar Gombe, Kabiru Jafaru, ya shaida wa Manema labarai cewa ɗan achaban yananan cikin ƙoshin lafiya, kuma tuni aka soma yaɗa bidiyon da ya yi jawabi da kan shi.
Hukumar ƴansanda ta roƙi jama’a su guji yaɗa labaran ƙarya, tare da shirin hukunta duk wani jami’in ta da ta samu da cin zarafin wani ko keta dokokin aiki sa


