Iran ta harbo jiragen yakin Amurka guda biyu cikin kasar da kuma a yankin Gulf a jiya jumm’a, kamar yadda jami’an Iran da Amurka suka fada, an ceto matuka jiragen su biyu, amma har yanzu ba gano na ukun su, wadda dakarun Iran suke farautarsa.
Lamarin ya nuna kasadar da jiragen yakin Amurka da Isra’ila suke fuskanta duk da ikirarin da shugaban Amurka Donald Trump, da sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth suka yi cewa dakarunsu ne suke da iko da sararrin samaniyar Iran.
Jirgi na farko, samfurin F15E ne mai wurin zaman mutane biyu, wadda Iran ta harbo shi kamar yadda jami’ai daga kasashen biyu suka fada.
Jirgi na biyu samfurin A-10 ne, wadda shima wuta daga Iran ne ya kakkapo shi, ya fadi a Kuwait, matukin jirgin yayi amfani da laimar tsira, kamar yadda Jami’an Amurka biyu suka fada.
Jiragen yakin Amurka biyu masu saukar Ungulu da suke aikin ceton matukin jirgin da suke nema, suma sun Iran ta kai harbe su, amma sun samu fita daga sararin samaniyar Iran, kamar yadda jami’ai biyu suka fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.


