Isra’ila tana shirin ta kai hari kan cibiyoyin makamashin Iran, amma tana dakon Amurka ta daga mata hanu tukuna, kamar yadda wani jami’in tsaro na Isra’ila ya fada a ranar Asabar, ya kara da cewa babu mamaki idan ta fara kai hare haren cikin mako mai zuwa.
Wannan furucin yana zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya baiwa Tehran wa’adin sa’o’i 48 ga Iran, wadda ya kare nuna ko Washington zata goyi bayan karin matakin sojin Isra’ila kan Iran.
Ahalinda ake ciki kuma, rundunar mayakan Iran, a cikin wata sanarwa data bayar yau Asabar, tace hana zirga zirga a mashigin ruwan Hormuz bai shafi makwabciyarta kasar Iraqi ba.


