Jami’an tsaro a Najeriya suna farautar gungun wasu ‘yan bindiga wadanda suka kama mazauna wasu kauyuka da yawa a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar, kamar yadda ‘yan sanda suka fada, wanda shine wani hari mafi muni na baya bayan nan a yankin.
‘Yan bindigar sun afkawa kauyukan Kurfa Danya, da kurfan Magaji da suke yankin Bukuyum a ranar Alhamis, suka bude wuta kan gidaje da motoci, kamin da suka rarake su kamar yadda wani jami’in karamar hukuma a yankin ya fada.
Shugaban karamar hukumar yankin Umar Abubakar Faru, ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, ‘yan bindigar sunyi awon gaba da mutane fiye da 150, galibin su mata da yara suka nufi dazukan da suke yankin, lamari da ya tilastawa mazauna kauyukan suka gudu, wadda ya maida kauyukan kusan kufayi.
Rundunar ‘Yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma ta ce har yanzu ana kan tantance yawan mutane ‘yan bindigar suka kama.
A wata sanarwa da rundunar ‘Yan sandan ta bayar, tace an tura wata rundunar hadin guiwar ‘Yan sanda da sojoji da wasu jami’ai daga wasu hukumomin tsaro, suna bin sawun ‘yan bindigar.
Rundunar ‘Yan sandan tace wasu mazauna yankin da suka tsere zuwa wasu sassa, an kai su asibiti, yayinda ake ci gaba da aikin ceton wadanda aka kama ake garkuwa da su.


