Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Janar Christopher Zai Maye Gurbin Ministan Tsaron Najeriya
Published: December 2, 2025 at 2:30 PM | By: Yusuf Aliyu Harande | Updated: December 2, 2025

Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Christopher Musa domin zama Ministan Tsaron kasar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya mika sunan tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, ga majalisar dattawa domin tabbatar da shi a matsayin sabon Ministan Tsaro, bayan murabus da Alhaji Mohammed Badaru Abubakar yayi jiya.

A wata wasika da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, shugaba Tinubu ya ce nadin Janar Musa ya biyo bayan ajiye aiki da Badaru ya yi a ranar Litinin saboda matsalolin lafiya.

Janar Musa, mai shekaru 58 da haihuwa a ranar 25 ga Disamba, ya kasance ɗaya daga cikin manyan hafsoshin soja da suka yi fice a ayyukan soja tun bayan shiga rundunar a shekarar 1991. Ya kasance Babban Hafsan Tsaro daga 2023 zuwa watan Oktoban 2025, tare da samun kyaututtuka da dama ciki har da Colin Powell Award for Soldiering a 2012.

An haife shi a Sokoto a 1967, inda ya yi karatunsa na firamare da sakandire, kafin ya tafi Kwalejin Nazari ta Zariya. Daga nan ya shiga Makarantar Horar da Sojoji ta NDA a 1986, inda ya kammala digirinsa a 1991.

Tun daga lokacin, Janar Musa ya rike mukamai da dama a rundunar soja, ciki har da Babban Jami’i mai lura da horo da ayyuka a Hedikwatar Runduna ta 81, Kwamandan Bataliya ta 73, da Mataimakin Darakta a Sashen Tsare-tsaren Runduna.

A 2019 ya jagoranci Sector 3 na Operation Lafiya Dole da kuma Multinational Joint Task Force a yankin Tafkin Chadi. Daga bisani, a 2021, aka nada shi Kwamandan Operation Hadin Kai, sannan ya jagoranci Rundunar Infantry kafin Shugaba Tinubu ya nada shi Babban Hafsan Tsaro a 2023.

A wasikar da ya aika majalisa, Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Janar Musa zai kara karfafawa Ma’aikatar Tsaro gwiwa tare da taimaka wa gwamnati wajen inganta tsaron kasa.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Iran Ta Tasa Keyar Wani Jirgi Shake Da Mai
Next Post: Tinubu Ya Maye Gurbin Badaru Da Tsohon Soja

Karin Labarai Masu Alaka

An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kotun Tarayya Ta Yankewa Nnamdi Kanu Daurin Rai-da-Rai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Sako Ɗaliban Makaranta 130 Da Aka Sace A Jihar Neja  Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ahmed Musa, Yayi Ritaya A ƙwallon ƙasa Da ƙasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Wani Jirgin Kasa Yayi Hatsari A Kudancin Spain Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Kasar Zimbabwe Ta Samar Da Dokar Tsawaita Mulkin Mnangagwa Zuwa 2030
  • ‘Yan Bindiga Sun Karya Alkawarin Dakatar Da Kai Hare Hare A Najeriya
  • Amurka Zata Bawa Sojojin Najeriya Horo
  • Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza
  • Shugabannin Kasar Australia Sun Bukaci ‘Yan Kasar Suyi Zanga Zanga Cikin Lumana

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Kasashen Cambvodia Da Thailand Sun Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsaro
  • ‘Yan Uwan Wadanda Aka Kashe Sunkai Kara Kotu Amurka
  • Babangida: Hakika Abiola Ya Lashe Zaben Watan Yuni 1993 Labarai
  • CAF Ta Dakatar Da Kocin Senegal Pape Thiaw Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kamfanin Jiragen Saman Ethiopia Zai Kafa Babban Filin Jirgi Afrika
  • Masu Kare Hakkin ‘Yan Gudun Hijira A Amurka Sun Mika Koke Amurka
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Alhamis 11.20.2025 Rediyo
  • Rasha Ta Nuna Kudurin Cimma Zaman Lafiya Da Ukraine Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.