A yayin da Sojojin Najeriya ke ikirarin samun nasarar fatattakar ‘yan bindiga a yankin Sakkwato dake Arewa Maso yammacin Najeriya, yankin tsakiayar kasar al’umma yankin ke ci gaba da kokawa akan yadda ‘yan fashin Dajin ke addabar jama’a.
Tsohon Gwamnan Kano na mulkin Soja Kanal Sani Bello Mai Ritaya, yace lamarin fa ba karamin rashin hankali bane bisa la’akari da yadda ‘yan fashin dajin suka zagaye Mahaifarsa ta Kontagora, duk kuwa nan hedikwatar Bada horo ta musamman ga rundunar Sojin Najeriya take.

To Matakin yin sulhu yana iya kawo saukin lamarin, Kanar Sani Bello, yace ya yadda da yin sulhu, amma idan suma ‘yYan bindigar zasu bayar da Makamansu.
Yanzu haka dai yankin na Arewacin Jihar Neja na ci gaba da gudanar da addu ‘o’i na musamman domin neman sauki daga Allah, akan wannan tashin hankali na ‘yan bindigar.


