Wakilin GTA Hausa “Amurka Ke Magana” a Gombe, Aliyu Bala Gerengi, ya rawaito cewa gobarar ta tashi ne a daren ranar Litinin, inda ake zargin matsalar lantarki ce ta haddasa ta, lamarin da ya jawo konewar shaguna da dama da kuma kayayyaki da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
Wannan iftila’i ya faru ne kwanaki 29 kacal bayan da wani ɓangare na kasuwar, musamman sashen tsofaffin ƙarafa da soso (scrap da metal), ya ƙone a ranar 17 ga Nuwamba, inda gobarar ta lalata shaguna fiye da 30 tare da dukiyoyi da aka kiyasta darajarsu ta haura naira miliyan 500.
A daren Litinin ɗin, wani ɓangare na kasuwar ya sake kamawa da wuta, abin da ya ƙara tsananta asarar da ’yan kasuwar suka tafka, musamman waɗanda itace kawai hanyar cin abincin su.
Amma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan gobarar da ta tashi a kasuwar katako a jihar, wacce ta ƙone shaguna da kayayyaki masu yawa, lamarin da ya janyo asarar dukiya mai yawa ga ‘yan kasuwa da dama.
Gwamnan Inuwa Yahaya, ya bayyana alhini da jimami matuƙa bisa faruwar wannan lamarin.
A cikin wata sanarwa da Darakta-janar na harkokin yaɗa labarai na gwamnatin jihar, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi da juyayi ga al’ummar da abin ya shafa, tare da miƙa saƙon jaje ga dukkan ‘yan kasuwa da masu shagunan da gobarar ta rutsa da su.
Sanarwar ta ce “Gwamna Inuwa ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa gwamnatin jihar tana tare da su a wannan lokaci na radadi, inda ya umarci hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar wato (SEMA) da sauran hukumomi masu alaƙa da su da su hanzarta bincike kan musabbabin gobarar, tare da kai tallafi da agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.
Gwamnan ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kafa wata cibiyar kwana-kwana ta zamani mai kayan aiki da ƙwarewa domin ƙarfafa kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.


