A ranar Alhamis, kasar Amurka ta saka sabbin takunkumi kan kasar Venezuela, inda ta kafa doka kan ‘yan uwan uwargidan shugaba Nicolas Maduro su uku da kuma takunkumi kan tankokin dakon mai da kamfanonin dake da alaka da su, yayin da Amurkan ke ci gaba da matsin lamba ga Caracas, fadar shugabancin Venezuela.
Daukan matakin ya biyo bayan da Amurka ta girke dakarun soja da dama yankin na kudancin karibiyan, kuma yayin da shugaba Doald Trump ke yakin neman hambarar da Maduro. Trump ya ce Amurka ta kame wani jirgin dakon mai da aka sawa takunkumi a gabar kogin Venezuela.
A wata sanarwa sashen kula da baitul malin Amurka, ta ce ta kakaba takunkumi kan kamfanoni 6 masu dakon man Venezuela, da kuma wasu tankokin dakon mai su shida, wanda ta ce suna aikata magudi, da matakan da zasu iya cutarwa, kuma suna ci gaba da samar da kudade da ke taimakawa mulkin Maduro na magudi da ta’addanci.


