Ƙasashen Amurka, Israel da Iran sun amince da tsagaita wuta na makonni biyu, an cimma yarjejeniyar ne biyo bayan shiga tsakani da Pakistan ta yi. Ana kuma sa ran jami’an Amurka da na Iran za su gana a ranar Juma’a domin tattauna hanyoyin samar da mafita ta dindindin.
Duk da cewa Tehran da Washington sun amince su fara tattaunawa, akan shawarwarin Iran guda 10 waɗanda Shugaban Amurka Donald Trump yace suna bayar da “ginshiki mai yiwuwa” na tattaunawa suna da ƙarancin kamanceceniya da shirin na kudurori 15 da Amurka ta gabatar a baya, abin da ke nuna cewa akwai manyan gibi da za a cike.
Misali, shirin Iran ya ƙunshi buƙatar ci gaba da tace uranium, abin da Amurka ta taɓa ƙin amincewa da shi. Haka kuma, waɗannan matakai 10 ba su tabo batun ƙarfin makamai masu linzami na Iran ba, wanda Israel da Amurka suka ce dole ne a rage su sosai.
Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ne ya sanar da tsagaita wutar tsakanin Iran da Amurka a dandalin X, inda ya ce ɓangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta nan take a ko’ina, ciki har da Lebanon, inda Isra’ila ta kai hare-hare.
Sai dai firaministan bai ambaci kudurorin Iran guda 10 ko shirin Amurka mai kudurori 15 ba, kuma sanarwar tasa ba ta yi magana kan wata yarjejeniya da Isra’ila ba.


