Kotu ta bayar da belin Abubakar Malami, dansa da matarsa akan naira miliyan N500 kowanen su.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon Antoni Janar na Tarayyar Najeriya, Abubakar Malami (SAN), tare da ɗansa Abubakar Abdulaziz Malami da kuma matarsa Bashir Asabe.
A hukuncin da alkalin kotun, Emeka Nwite, ya yanke a ranar Laraba, kowannen su ya samu beli ne a kan kuɗin naira miliyan 500.
Ana ci gaba da sauraron shari’ar da ta shafi zarge-zargen cin hanci da rashawa da karkatar da kuɗin gwamnati.


