Wata kotun soja a kasar Rasha ta yanke hukumcin daurin shekaru 22 a gidan kurkuku a kan wani dan kasar Belarus wanda hukumar tsaron cikin gida ta Rasha ta ce ya kai harin bam a kan wasu jiragen kasar biyu a yankin Siberiya, bisa umurnin hukumar leken asirin kasar Ukraine.
Ofishin gabatar da kararraki ta Rasha ta fada yau alhamis cewa an samu Sergei Yeremeyev da laifin ta’addanci ta hanyar dasa bama-bamai a wasu jiragen kasa na daukar kaya biyu a shekarar 2023.
Hukumar tsaron cikin gidan Rasha ta fada a lokacin da aka kama shi cewa ya amsa laifinsa.
Hukumar leken asirin Ukraine ta ce ita ce ta shirya kai hare-haren biyu a yankin Buryatia dake bakin iyaka da kasar Mongoliya, wanda kuma dubban kilomitoci daga bakin iyakar Ukraine, amma hukumar leken asirin ta Ukraine ta fada a lokacin cewa tana kokari ne ta gurgunta zirga zirgar jiragen kasa a Siberiya wanda ta yi ikirarin cewa Rasha na amfani da su wajen jigilar kayayyakin yaki.


