Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Kotun Tarayya Ta Yankewa Nnamdi Kanu Daurin Rai-da-Rai
Published: November 20, 2025 at 5:25 PM | By: Yusuf Aliyu Harande | Updated: November 21, 2025

Wata kotu a Najeriya ta yanke hukumcin daurin rai da rai a gidan kurkuku, a kan madugun kungiyar ‘yan awaren nan ta Biafra, ta kudu maso gabashin Najeriya, Nnamdi Kanu, bayan da ta same shi da dukkan laifuffuka guda 7 da aka tuhume shi da aikatawa da suka shafi ta’addanci.

Mai shari’a Ja’es Omotosho na babbar kotun tarayya dake Abuja, yace masu gabatar da kararraki sun tabbatarwa kotun cewa irin kalamun da yayi da aka watsa ta kafar rediyo da kuma umurnin da yayi ta ba magoya bayan kungiyarsa ta “Indigenous People of Biafra” ko IPOB a takaice, sun haddasa kai munanan hare-hare da suka janyo hasarar rayukan jami’an tsaro da fararen hula.

Wannan zub da jinin wani bangare ne na yunkurin da yake jagoranta na kawowa ga ballewar yankin da mafi yawan al’ummarta ‘yan kabilar Igbo ne. A shekarar 1967, yankin yayi yunkurin ballewa ta hanyar ayyana Jamhuriyar Biafra, abinda ya haddasa yakin basasar shekaru uku, inda mutane fiye da miliyan daya suka mutu.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Jihar Kano Zata Kashe Makudan Kudade Ga Jama’ar Kano!
Next Post: Shirin Dare 2030 UTC Yau Alhamis 11.20.2025

Karin Labarai Masu Alaka

Ministan Tsaron Najeriya Badaru Yayi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaba Tinubu Ya Kara Aika Sunayen Jakadu Ga Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Tabbas Atiku Abubakar Ya Karbi Katin Jam’iyyar ADC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
‘Yan Bindiga Sun Kama Akalla Mutane 13 A Wani Coci A Jihar Kogi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Yau Shekaru 60 Da Kisan Gilla Ga Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Gwamnatin Najeriya Na Shirin Yin Zamiya Don Biyan Bashi Labarai
  • Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Ziyarci IBB Siyasa
  • NAHCON Tafara Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026 Najeriya
  • Kudi Sunfi Rayuwar Mutum Muhimmanci A Asibitocin Najeriya Kiwon Lafiya
  • An Saka Dokar Hana Fita A Karamar Hukumar Lamurde Jihar Adamawa Tsaro
  • Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha: Tura Sojojin Birtaniya Ukraine Zai Kara Ta’azzara Yaki Labarai
  • Tinubu Yace Zayyi Hadaka Da Kasashen Duniya Domin Kawo Karshen Rashin Tsaro. Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.