Kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS ta yi ikirarin daukar alhakin harin da aka kai sansanin sojin jiragen sama na kasar Niger da tsakar daren ranar Alhamis, inda aka jikkata Sojoji 4, aka kuma lalata wani jirgin sama.
Ikirarin alhakin kai harin ya fito ne ta gidan yada labarai na Amsaq, kafar da ‘yan ta’addan ke yawan amfani da wajen yada farfagandar su. Sun ce harin na bazata ne, kuma an tafka barna da yawa.
Gidan Talabijin na kasar Niger kuma ya ruwaito cewa dakarun sojin kasar sun mai da martani kan harin nan da nan, inda suka kashe mahara 20, suka kuma kama wasu 11.
Hoton videon da aka dauka ya nuna tartsatsin wuta da karar fashewar bomb, a harin da aka fara kaiwa da tun tsakar dare, aka kuma shafe awanni biyu a kai, a wajen filin jirgin sama na Diori Hamani da ke Niamey, babban birnin kasar Niger.


