An kashe sojojin Amurka biyu da wani farar hula ba Amurke daya, yayin da aka raunata wasu mutanen uku a lokacin da wani dan kungiyar ISIS yayi musu kwanton bauna ya bude musu wuta a yankin tsakiyar kasar Sham, watau Syria a yau din nan.
Wannan shine harin farko da ya haddasa mutuwa da aka kai kan sojojin Amurka a kasar ta Sham tun daga lokacin da aka hambarar da gwamnatin Shugaba Bashar al Assad shekara guda da ta shige.
Rundunar sojojin Amurka a yankin gabas ta tsakiya ta ce domin mutunta ‘yan’uwan mamatan, ba zata bayyana sunayensu ba har sai bayan sa’oi 24 da sanar da su.
Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya rubuta a shafin X cewa duk wanda ya kai hari ya kashe Amurkawa a ko ina yake a duniya, zai shafe sauran ‘yan kwanaki kalilan da suka rage masa a duniya da sanin cewa Amurka zata farauto shi, ta hallaka shi.
Kamfanin dillancin labarai na kasar Sham, SANA, ya fada tun farko cewa wannan harin da aka kai a kusa da kangon birni mai tarihi na zamanin da da ake kira Tadmur, ko Palmyra a turance, yayi sanadin raunata wasu sojojin Sham guda biyu da wasu na Amurka da dama.
SANA yace an kashe maharin ba tare da ba da karin bayani ba amma kungiyar sa’ido kan al’amuran kare hakkin bil Adama a Sham mai hedkwata a Britaniya, ta ce maharin sojan kasar Sham ne.
Amurka tana da daruruwan sojojin da ta girka a gabashin kasar Sham a wani bangare na gamayyar yaki da ‘yan ISIS


