Mambobin Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) sun hallara a Sakatariyar NLC, wato Labour House da ke Abuja, a ranar Laraba, domin gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya kan ƙaruwar matsalar tsaro da kuma tabarɓarewar halin tattalin arziki a faɗin ƙasar.

Shugaba Bola Tinubu ya gana da shugabannin NLC a daren ranar Talata, a ƙoƙarin dakatar da zanga-zangar, sai dai Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya shaida wa ‘yan jarida cewa ba a cimma wata matsaya da za ta hana gudanar da ita ba.
Daga cikin waɗanda suka halarci zanga zangar akwai Shugaban NLC, Joe Ajaero, da kuma ƙungiyoyin farar hula, ciki har da Omoyele Sowore da takwarorinsa daga ƙungiyar Revolution Now Movement.


