Gabannin zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) za ta gudanar a yau laraba, rundunar ‘yan sanda ta tura jami’an tsaro na musamman domin tabbatar da zaman lafiya da hana tashin hankali.

NLC ta jaddada cewa ba za ta janye zanga-zangar ba, wadda aka shirya sakamakon tabarbarewar tsaro, tsadar rayuwa, da sauran matsalolin ma’aikata.
Kakakin ƙungiyar, Benson Upah, ya yi gargaɗi cewa duk wani yunƙurin kawo cikas ko cutar da ko da mutum ɗaya zai iya haifar da yajin aikin ƙasa baki ɗaya na dindindin.
Ƙungiyar ta ce ta samu bayanan sirri na yiwuwar shigar ‘yan daba ko ‘yan siyasar haya cikin zanga-zangar, tare da kiran mambobinta da al’umma su kasance cikin lumana da haɗin kai.
NLC ta bayyana zanga-zangar a matsayin matakin ‘yan ƙasa gaba ɗaya na neman ingattaccen tsaro da gyaran shugabanci, tana mai kira ga ‘yan sanda su kare ‘yancin jama’a na taruwa don bayyana koke-koken su bisa dokar kasa.


