NEC Ta Nada Gwamna Nasir Idris Shugaban Kwamitin Raya Kiwo
Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya (NEC) ta nada Gwamnan jihar Kebbi, Comrade Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu), a matsayin shugaban sabon kwamitin raya harkar kiwo a Najeriya.
An yanke wannan hukunci ne a taron NEC karo na 155 da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya jagoranta, inda ya ce nadin na da nufin samar da mafita mai ɗorewa ga rikicin manoma da makiyaya da kuma tabbatar da wadatar abinci.
Kwamitin zai duba shawarwarin gyaran kiwo, ya tantance jihohin da ke da sha’awar aiwatar da shirye-shiryen raya kiwo, tare da haɗa gwiwa da Ma’aikatar Raya Kiwo.
Mataimakin Shugaban Ƙasa ya tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta bai wa shawarwarin kwamitin kulawa ta musamman domin bunƙasa tattalin arziki da samar da zaman lafiya.


