Nan bada jimawa ba Makarantun Allo zasu yi gogayya da takwarorinsu na Boko dake faɗin Kasa. ”in ji Minitan Ilimi na Tarayyar Najeriya.
Ministan Ilimin Najeriya Dakta Tunji Alausa yace tsarin ingatawa tare da koyar da Karatun Allo da ilimin Tsangayu dake da manufar inganta karatu da rayuwar Almajirai da aka kaddamar ranar Litinin din data gabata, manufar samar da tsarin bai daya da za a rinka amfani da shi a matakin kasa baki daya.

Da yake karin haske dangane da wannan gagarumin sauyi da ma’aikatar ilimin ke kokarin aiwatarwa, maitaimakawa Ministan ilimin Najeriya kan ilimin Almajirai da Tsangayu hadi da makarantun Allo, Dr. Balarabe Shehu Kakale, Barden Tsangayu da Makarantun Allo na Kasar Hausa yace nan bada jimawa ba Makarantun Allo zasu yi gogayya da takwaroinsu na Boko dake faɗin kasar.
Haka zalika, Dr. Kakale, ya kara da cewa kafin akai ga wannan matsayar, sai da suka karade daukacin shiyyoyin siyasa shida na Najeriya inda suka tattauna da masu ruwa da tsaki da suka hada da Malamai da sarakuna da Kungiyar kiristoci ta Najeriya wato CAN, sai dai ya bayyana bukatar dake akwai wajen ganin gwamnatocin jihohi sun kara damba domin kaiwa ga cikakkiyar Nasara.

Tun da fari, Dr. Balarabe Shehu Kakale tsohon danmajalisar tarayya Najeriya, ya yabawa Ministan ilimin Najeriya Dakta Tunji Alausa da Ministan kasa a ma’aikatar ilimin kasar Dr. Suwaiba Ahmed da kuma shugaban hukumar kula da ilimin Almajirai da yara da basa zuwa makaranta ta kasar Dr. Mohammed Sani Idris hadi da jagororin addinai da sarakuna bisa matakan da suke dauka na inganta ilimin Almajirai dama rayuwar yaran da basa zuwa makaranta ta hanyar koyar da su sa’o’in hannu da zai basu damar dogaro da kan su.


