Ruben Amorim ya bar matsayinsa na Babban Kocin ƙungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United.
An nada Ruben a watan Nuwamba na 2024 kuma ya jagoranci kungiyar zuwa wasan karshe na UEFA Europa League a Bilbao watan Mayu inda ta zo na biyu bayan Tottenham ta doke ta 1-0.
Yanzu haka ƙungiyar ta Manchester United tana matsayi na shida a teburin gasar Firimiyar Ingila na bana.
Shugabannin gudanawar kungiyar sun yanke shawarar cewa lokaci ya yi da ya dace a yi sauyi.
Wannan zai bai wa kungiyar damar kammala gasar Firimiyar cikin yanayi mafi kyau.
Kungiyar ta gode wa Ruben saboda gudunmawar da ya bayar ga kungiyar kuma tana yi masa fatan alheri a nan gaba.
Tsohon dan wasan Manchester United Darren Fletcher shi zai jagoranci kungiyar a wasan da za ta fafata da Burnley a ranar Laraba.


