Matatar Man Dangote ta ƙarfafa matsayinta a matsayin babbar cibiyar rarraba man fetur a Nijeriya, bayan rage farashin man zuwa naira ₦699 kan kowace lita da kuma sauƙaƙa mafi ƙarancin adadin saye daga lita miliyan 2 zuwa lita 250,000.

Matakan sun ja hankalin ’yan kasuwar man fetur a faɗin ƙasar, inda ake samun fiye da motoci 1,000 na ɗaukar man a kullum daga matatar.
Kamfanin ya kuma ƙaddamar da tsarin garantin banki na kwanaki 10 domin tabbatar da wadatar kaya ba tare da tsaiko ba.
Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote, ya ce manufar kamfanin ita ce samar da makamashi mai rahusa kuma mai sauƙin samu ga kowane ɗan Nijeriya, yana mai jaddada cewa aikin matatar ya fi karkata ne kan bunƙasa ƙasar fiye da neman riba.
A nasu ɓangaren, Kungiyar ’Yan Kasuwar Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Nijeriya (IPMAN) ta yi kira ga mambobinta su rika sayen man daga Matatar Dangote, tana mai tabbatar da cewa ba za a samu ƙarancin man fetur ba, duba da yadda kungiyar ke rike da sama da kashi 80 cikin 100 na kasuwar sayar da mai a fadin ƙasar.


