Mawakiya Cardi B ta sauya yanayin shigar ta, yayin da take ta yabon Saudi Araibiya, tana cewa “komai masha Allah.”
Bidiyon da mawakiya Cardi B ta yi yayin da take wasa a Riyad babban birnin Saudiya da sanyi safiyar Lahadi ya yadu sosai, inda mawakiyar ta ke ta yabon kasar, a shafin ta na Instagram, tana cewa komai sabo ne a wannan kasa, kamar jiya aka bare ta daga leda.
Mawakiyar na daya daga cikin manyan ‘yan wasa da suka baje kolin su a wasan MDLBEAST a Riyadh, inda ta yiwa dubban mutanen da suka halarci wajen maraba da sallama irin ta addinin musulunci. “Assalamu Alaikum,” sannan kuma ta ce komai masha Allah.
A waken nata da take yi, Cardi B ta ajiye tsauraran kalamai, kuma ta yi shiga irin ta kamala, inda ta rufe duk sassan jikin ta, abin da ya bambanta da yadda ta saba.


