Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Mayakan Boko Haram Da ISWAP Sun Kai Hari Cikin Dare
Published: April 10, 2026 at 9:50 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A Najeriya gamayyar mayakan kungiyar Boko Harama da ISWAP sun kai hari na hadin baki cikin dare kan sansanoni daban daban a jihar Barno, har suka kashe wani janar da wasu sojojin kasar, kamar yadda wasu majiyoyin soji suka fada ranar Ahamis.

Helkwatar mayakan kasar, sunce mayakan sun kai hari kan wata cibiyar sojoji da ke Benisheikh amma aka taka musu birki, ta tabbatar da an kashe sojoji a artabun, helkawatar ta bukaci jama’a su dakaci karin bayani dangane da wadanda rikicin ya shafa.

Mayakan sun fara kai hari ne kan garuruwan Pulka, da Bakin ruwa wadanda suke karamar hukumar Gwoza a daren laraba, sannan suka yi kokarin kama helkwatar runduna ta musamman ta 29 dake Benisheikh da tsakar dare, inji helkwatar ta mayakan Najeriya. Ta kara da cewa sojojin Najeriya suka ja daga karkashin jagorancin janar Oseni Braimah suka fatattaki ‘yan bindigar.

Sai dai wasu majiyoyin soja biyu sun fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, ‘yan bindigar sunyi dai dai da sansanin da yake Benisheikh, suka kashe janar Oseni Braimah, da wasu sojoji cikin su har da wani mai mukamin keftin, suka lalata motocin soja masu yawa. Kamfanin dillancin labarai na Reuters bashi da tabbaciin wannan labari.

Wani jami’in soja, wanda yana daga cikin wadanda suka kai dauki a Benisheikh, yace jiragen yaki ta sama su suka yi jigilar wadanda suka kwanta dama a harin na Benisheikh a ranar Alhamis, bayanda suka taimaka wajen korar ‘yan binidgar wadanda suka yi sa’o’I uku suna barna a yankin.

Ahalinda ake ciki kuma, rassan kungiyoyin al-qeada da ISIS a yammacin Afirka a karon farko sun baiwa hamata iska a Nijar, kamar yadda wata sanarwa da daya daga cikin kungiyoyin ta bayar, mataki a masu fashin baki suka ce ya karfafa gababar da take tsakanin kungiyoyin na shekara da shekaru.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Birtaniya Zata Hana Jiragen Ruwan Rasha Wucewa
Next Post: Kasuwannin Hannun Jari Sun Farfado

Karin Labarai Masu Alaka

Hari Akan Wata Mashaya Ya Rutsa Da Mutane 9 A Afirka Ta Kudu Afrika
An Kama Tsohon Jakadan Birtaniya A Amurka Peter Mandelson Amurka
Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Yace Rasha Tana Cin Ribar Yakin Gabas Ta Tsakiya Afrika
Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
Jami’an Tsaron Pakistan Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Labarai
Jagoran Kwankwasiya A Najeriya Ya Koma Jam’iyar ADC Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Hari Da Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Mutane Da Dama A Darfur
  • Ana Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Djibouti Yau Juma’a
  • Farashin Man Fetur Yakara Tashi
  • Kasuwannin Hannun Jari Sun Farfado
  • Mayakan Boko Haram Da ISWAP Sun Kai Hari Cikin Dare

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Gana Da Shugaba Tinubu Siyasa
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria Siyasa
  • Hanyar Gombe Dukku Darazo Ta Zamo Abun Damuwa Ga Al’ummar Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • Najeriya Ta Kai Wasan Kusa Da Na Karshe A Wasan Dambe Na Matasan Afirka Wasanni
  • Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi Labarai
  • Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya Afrika
  • Dan Gudun Hijira Tarique Rahman Ya Kusa Zama Shugaban Kasa Labarai
  • Karo Na Biyu Cikin Kwanaki 29 An Samu Gobara A Kasuwar Katako Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.