Ministan Kudi da tsara tattalin arzikin Najeriya Wale Edun, ya ce gwamnatin tarayya ba ta cimma burin kudaden shiga na shekarar 2025 ba, sabanin ikirarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Edun ya bayyana cewa gwamnati ta yi hasashen samun naira tiriliyan 40.8 a 2025, amma zuwa yanzu an samu kusan naira tiriliyan 10.7 kacal.
Ya ce gibin kudaden shiga ya samo asali ne daga raunin kudaden man fetur da iskar gas, da kuma rashin tabbas a wasu bangarorin kudaden shiga marasa alaka da man fetur.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani zama da kwamitocin Majalisar Wakilai kan Kudi da Tsare-tsaren Kasa, inda aka tattauna Tsarin Kashe Kudi na Matsakaicin Lokaci na 2026–2028 (MTEF) da Takardar Dabarun Kasafin Kudi (FSP).
Ya kara da cewa sakamakon wannan gibi, gwamnatin tarayya ta karbi bashin kimanin naira tiriliyan 14.1 domin cike gibi, lamarin da ke kara tayar da hankula kan dorewar kudaden gwamnati.


