Murabus din Jami’an gwamnatin Bulgaria ranar Alhamis, a jajibirin shigar kasar yankin euro, ya kawo karshen mulkin da ke da bakinjini wajen al’ummar kasar, amma kuma yana iya jefa ta cikin ya mutsin siyasa na lokaci mai tsawo.
Bulgaria wadda memba ce ta Majalisar Turai da kuma NATO, ta gudanr da zabubbuka na kasa har sau 7 a shekaru hudu da suka gabata, yayin da gwamnati me ci ta kasa samun rinjaye a majalisun kasar.
Tun a watan Janairu, gwanatin mai barin gado ta so ayi bikin sanya kasar cikin yankin Euro, amma sai prime minister Rosen Zhelyakov ya mika takardar murabus bayan da aka shafe makonni ana zanga-zanga, kan cin hanci da rashawa na gwamnati, da kuma kasafin kudin da ta gabatar wanda zai karawa mutane haraji.


