Kungiyar kiristoci ta CAN a Nigeria tace yaran Makarantar St Mary na Garin Papiri ta jihar Neja da akayi Garkuwa dasu a cikin watan Nuwamban nan da yagaba suna cikin koshin Lafiya.
Mai Magana da yawun Kungiyar ta CAN a jihar Neja Mr. Dan Atori Yace a ranar Litinin lokacin da mai ba Shugaban Kasar Bola Tinubu shawara akan Lamarin Tsaro Malam Nuhu Ribado ya Kai ziyara a kontagora ya tabbatar Musu da cewa yaran suna cikin koshin lafiya Kuma ana nan ana kokarin karbosu Daga Hannun masu garkuwa dasu cikin koshin Lafiya.
Yace tun bayan ziyarar Nuhu Ribadu mu da uwayen Yara da Sauran Jama,a Muka Samu kwarin guiwa tare bayyana fatan cewa yaran Nan da malamans u zasu Dawo ga iyayen su.
To gwamnatin jihar Nejan dai tace Saboda akwai shakku akan yawan adadin yaran makarantar ta St da akace anyi garkuwa dasu yasa suka bude sashen yin rijista ga duk Wanda yasan yaron shi na ciki.
Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Abubakar Usman yace ya zuwa yanzu kuma yara 68 ne aka Samu.
Tunda farko dai kungiyar ta CAN tace sama da yara 300 ne aka dauka amma kuma Daga bisani CAN din tace yara 50 sun kubuta kuma sun mika su ga iyayen su ba tare da an nunawa hukumomi ko kuma manema labarai ba.


