Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Najeriya, Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 80, Sun Ceto 34
Published: December 29, 2025 at 4:42 PM | By: Bala Hassan

Sojoji sun hallaka ‘yan ta’adda sama da 80, sun ceto mutane 34 a jihohi da dama

Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun hallaka ‘yan ta’adda sama da 80, tare da ceto mutane 34 da aka sace, a jerin hare-haren haɗin gwiwa da aka gudanar tsakanin ranakun 25 zuwa 29 ga Disamba, 2025.

Wata majiya mai tushe daga Hedkwatar Sojin Ƙasa ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa an samu waɗannan nasarori ne a jihohin Borno, Adamawa, Sokoto, Katsina, Neja, Zamfara, Filato, Delta, Cross River da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).

A jihar Borno, majiyar ta ce hare-haren sama tare da bin diddigi na ƙasa da aka kai a Sowolwolo, cikin Ƙaramar Hukumar Bama, da kewayenta, sun yi sanadin hallaka ‘yan ta’adda 19, tare da rusa sansanonin ajiyar kayayyakin su da tarwatsa hanyoyin sadarwar ISWAP da JAS.

Ta ƙara da cewa wasu hare-hare na gaba da aka kai a yankunan Gulumba Gana, Kumshe, Kasho Miri da Chongolokura sun yi sanadin hallaka ƙarin ‘yan ta’adda 38. Haka kuma, bayanan leƙen asiri da sa ido (ISR) sun gano manyan shugabannin ‘yan ta’adda da ake shirin kai musu hari nan gaba.

A jihohin Neja da Katsina kuwa, majiyar ta bayyana cewa dakarun soji sun fatattaki hare-haren ‘yan ta’adda da aka kai sansanin FOB Kwanar Dutse a Ƙaramar Hukumar Mariga, da kuma kan hanyar Shanono–Katsina. A yayin wannan samame, an ceto farar hula guda ɗaya tare da ƙwato shanu 78 da tumaki 28 da ‘yan ta’addan suka sace.

Game da ayyukan ceto daga hannun masu garkuwa da mutane, majiyar ta ce a jihar Kebbi, dakarun Bataliya ta 223 sun ceto mutane 16 bayan samun bayanan sirri a ƙauyen Unashi da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu.

A jihar Filato kuma, an ceto mutum guda a yankin Yaka Naji Jandutse da ke Ƙaramar Hukumar Wase.

Majiyar ta ƙara da cewa dakarun sun kuma dakile ayyukan ta’addanci da laifuka a sassa daban-daban na ƙasar, inda suka cafke masu haƙar ma’adinan zinare ba bisa ƙa’ida ba guda 11 a birnin Tarayya Abuja. Haka kuma, an kama wasu mutane biyu da ake zargi da fashi da makami a Filato, tare da kwato kuɗaɗen da suka sace.

A jihar Delta, an cafke masu satar ɗanyen mai guda biyu, inda aka ƙwato jarkoki 104 (lita 2,600) na ɗanyen mai. A Cross River kuwa, an kama wasu da ake zargin ‘yan fashin teku nr mutum uku da ke da alaƙa da ƙungiyar ‘yan bindiga ta BIG JOE.

Majiyar ta jaddada cewa waɗannan ayyuka na nuna ƙudirin sojojin Najeriya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tabbatar da bin doka da oda, da kuma wanzar da zaman lafiya da tsaro a dukkan yankunan da abin ya shafa.

Ta kuma sake tabbatar da aniyar Rundunar Sojin Ƙasa ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa sahihan bayanan sirri, ceto waɗanda aka sace, da kuma murƙushe duk wata barazana daga ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a faɗin ƙasar.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Shahararren Dan Dambe Anthony Joshua Yayi Hatsarin Mota A Jihar Ogun
Next Post: Layin Raba Wutan Lantarki Na Najeriya Ya Fashe

Karin Labarai Masu Alaka

Aliko Dangote: Faruk Ahmed Ya Ci Amanar ‘Yan Najeriya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Farashin Dalar Amurka Ya Tashi Ranan Juma’a Amurka
NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaba Bola Tinubu Ya Tafi Turai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jihohin Arewaci Sun Kafa Asusun Yaki Da Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Tsofin Shugabanin Kasa Sun Karbi Bakoncin Hafsan Sojin Najeriya Tsaro
  • Margayi Shugaba Muhammadu Buhari 1942-2025 Labarai
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas Najeriya
  • Akwai Bukatar Hukunci Mai Tsanani Ga Duk Wanda Yayi Fyade Najeriya
  • Rasha Takai Mummunan Hari Birnin Kyiv Afrika
  • Anfara Kirga Kuri’a A zaben Kasar Guinea Labarai
  • CAF Ta Dakatar Da Kocin Senegal Pape Thiaw Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Gana Da Shugaba Tinubu Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.