Nigeria zata bude asusun dala bilyan biyu, domin samarda kudaden da kasar zata yi amfani da su wajen habaka sashin makamashi da bashi dogaro da mai.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda ya bayyana haka a ranar talata, yace dokin da masu zuba jari suka nuna wajen sayen hannayen jarin da kasar ta fitar a bangaren nan, ya nuna muhimmancin da aka azawa wannan fanni.
Da yake magana yau a Abu Dhabi a wani babban taro gameda muhalli da sakewar yanayi, shugaba Tinubu yace kasar tana da burin tara kudade dala milyan 500 domin samarda kayayyaki aiki da ingantawa, yayinda asusun bilyan biyu kuma, gwamnati zata yi amfani da su domin karfafawa ayyukan da ake yi domin rage hayaki da yake janyo dumamar yanayi da rage dogaro kan mai.
Haka nan Shugaba Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya da hadaddiyar daular larabawa, sun sanya hanu kan yarjejeniya mai karfi da zummar habaka cinikayya da kasuwani tsakanin kasashen biyu da za su shafi habaka hanyoyin samun makamshi da bai dogara akan mai ba,sufuri ta sama, da kasa, da noma, kasuwanci ta amfai da na’urori, da sauran su.
Najeriya tana Fuskantar kalubale ta fuskar manufofinta gamda muhallli, yayinda take kokarin daina kona iskar gas da danginsu, a kokarin da take yi na sake fasali domin rage dumamar yanayi.


