Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Kwamared Joe Ajaero, ya yabawa Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa irin kulawa da tabbatar da jin daɗin ma’aikata a jihar.
Ajaero ya bayyana hakan yayin wani taron da ya gudana, inda ya ce ko da yake ƙungiyar ba ta cika yawan yabon gwamnoni ba, amma Gwamna Inuwa Yahaya ya cancanci yabo bisa irin yadda yake baiwa ma’aikata muhimmanci da kuma cika alƙawurra.
Saboda haka, NLC ta karrama Gwamna Inuwa da lambar yabo ta “Gwamna Mai Ƙaunar Ma’aikata”, a matsayin wanda ke da kyakkyawar dangantaka da ma’aikatansa tare da ɗaukar walwalarsu a matsayin fifiko.
Wannan karramawa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Gombe ke ci gaba da aiwatar da manufofi da tsare-tsare da suka shafi ci gaban ma’aikata da inganta rayuwar su kamar aiwatar da mafi karancin albashi da kuma aza tubalin gida ofishin sakatariyar kwadago.


