Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Amurka Tayi Barazanar Zata Rage Tallafin Da Take BayarwaSudan Ta Kudu, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Nuhu Ribadu Ya Mika Dalibai 100 da Aka Ceto Ga Gwamnatin Jihar Neja
Published: December 8, 2025 at 7:24 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mai bada Shawara kan Tsaro ga Shugaban Ƙasa (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya mika dalibai 100 na makarantar St. Mary Catholic School da ke Papiri, karamar hukumar Agwara a jihar Neja, ga gwamnatin jihar bayan ceto su daga hannun masu garkuwa da mutane.

An gudanar da mika su a Minna a ranar Litinin, inda Wing Cdr. Abdullahi Idi Hong ya wakilci Nuhu Ribadu wajen gabatar da su ga gwamnatin jihar.

Hong ya ce ceton ya biyo bayan makonni na tsauraran hare haren hadin gwiwa tsakanin ofishin mai bawa shugaban kasa Shawara ta fannin tsaro, Hukumar DSS, Rundunar Sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro.

Ya bayyana cewa DSS ta taka “muhimmiyar rawa ta zahiri” a aikin da ya tabbatar da dawowar yaran cikin koshin lafiya.

Ya kara da cewa ofishin Nuhu Ribadu ya fara samar da matakan gaggawa na tsaro a yankunan da ke fuskantar barazana, tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi, shugabannin gargajiya da na addini domin samar da tsarin tsaro mai dorewa.

Hong ya jaddada cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da ke nufin tabbatar da tsaro a makarantu domin kare hakkin kowane yaro ya samu ilimi cikin kwanciyar hankali.

Da yake jawabi, Gwamna Umaru Bago ya bayyana wannan rana a matsayin “muhimmiya a tarihin jihar Neja,” inda ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa tallafin da ya bai wa hukumomin tsaro wajen cimma nasarar dawo da yaran.

Haka kuma ya yi godiya ga ofishin mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin tsaro, jami’an tsaro, hukumomi da al’ummar jihar da suka yi addu’o’i a lokacin da yaran ke hannu.

Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwa cewa sauran daliban da har yanzu ke hannun masu garkuwa za a kubutar da su ba da jimawa ba.

Ya tabbatar wa iyaye cewa za a mika yaran ga iyalansu bayan cikakken binciken lafiya.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida
Next Post: Dangantaka Tayi Tsamari Tsakanin Salah Da Slot.

Karin Labarai Masu Alaka

Wani Dan Bindiga Ya Harbi Dakarun Tsaron Cikin Gida Su Biyu A Washington DC Labarai
Gwamnan Jihar Gombe Ya Umurci A Rufe Makarantu Labarai
Ghana Ta Haramta Hakar Ma’adinai A Gandunan Dajin Data Kebe, Labarai
Mizanin Tattalin Arzikin Najeriya Na 2024 Ya Karu Da Kashi 3.84% Labarai
Kanal Sani: Idan ‘Yan-Ta’adda Zasu Mutunta Sulhu To Gwamnati Ta Duba Hakan Labarai
Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike a Tituna
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa
  • Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000
  • Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakuncin Wasannin Afirka Na 2031.
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Rediyo
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Gwamnonin Arewa “Mun Amince Da Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi” Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wasu Yara 50 Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai
  • GTA Hausa Logo
    Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakuncin Wasannin Afirka Na 2031. Wasanni
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Laraba 11.19.2025 Rediyo
  • Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa Afrika
  • Nasarawa Ce Zakara A Wasan Kwallon Kafa Ta Kurame 2025 Wasanni
  • An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.