Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), ya mika sauran dalibai da malamai 130 na Makarantar St Mary’s Private Catholic Primary and Secondary School da ke Papiri, karamar hukumar Agwara a jihar Neja wadanda suka samu ‘yancinsu a ranar Juma’a, ga gwamnan jihar, Umar Bago.

Rahotanni sun ce an kubutar da daliban ne a ranar Juma’a a tsakanin kananan hukumomin Agwara da Borgu na jihar.
Da yake jawabi a ranar Litinin a wani gajeren biki da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Minna, Ribadu, wanda Adamu Laka, mai kula da Cibiyar Yaki da Ta’addanci (CCT) ta Abuja ya wakilta, ya ce aikin ceto da ofishin NSA ya jagoranta ya yi nasara ne sakamakon hadin gwiwar hukumomin tsaro daban-daban, ciki har da Rundunar Sojin Najeriya, ‘yan sanda, da hukumar tsaro ta DSS.


