Shugabannin PDP sun nemi taimakon Obasanjo domin dawowar jam’iyyar kan mulki’ a 2027
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Taminu Turaki, ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta, Jihar Ogun, tare da wasu shugabannin jam’iyyar, na da nufin gabatar da sabbin shugabanni da kuma neman shawarwari gabanin zaben 2027.
Turaki ya ce sun nemi samun kwarin gwiwa da jagoranci daga Obasanjo, wanda ya bayyana a matsayin kwararren dattijo, domin karfafa jam’iyyar kafin manyan zabuka masu zuwa, ya kuma jaddada cewa PDP ta shirya tsaf domin karbar ragama a 2027.
Shugaban PDP ya bayyana cewa jam’iyyar na da yakinin lashe zabukan gwamna na Jihohin Ekiti da Osun, inda ya ce hakan zai nuna cewa PDP na kan dawowa domin kwato mulki daga APC a 2027.


