Ronaldo da Messi ka iya hadu a Gasar Cin Kofin Duniya: Ta yaya kuma a mataki zai iya faruwa?
A shirye-shiryen fafatawa a gasar cin kofin Duniya FIFA World Cup 2026, wadda kasashen uku da suka hada da Amurka Mexico da Kanada zasu karbi bakunci, ana hasashen fittatun manyan ‘yan wasan kwallon kafa na Duniya Leonel Messi dan kasar Argentina da Cristiano Ronaldo daga Putugal na iya haduwa da junan su a wani mataki in har sun nasara a wasannin su.

Lionel Messi yana neman lashe kofin duniya karo biyu da kuma bayyanarsa ta uku a wasan ƙarshe na babban gasar ƙwallon ƙafar duniya.

Shi kuwa Cristiano Ronaldo yana neman kaiwa ga wasan ƙarshe na farko a tarihin gasar cin kofin Duniya.
Ta Ya Ya Gwarzayen Biyu Zasu Iya Haduwa Da Junansu ?
Da farko, Messi da Argentina za su buƙaci lashe rukunin J. Waɗannan abokan hamayya sun haɗa da:
1. Algeria
2. Austria
3. Jordan
A gefe guda kuma, Ronaldo da Portugal za su buƙaci lashe rukunin K. Waɗannan abokan hamayya sun haɗa da
1. Uzbekistan
2. Colombia
Kasar da ta samu nasara a wasan cike gurbi na fifa rukunin 1
Daga nan, Argentina da Portugal za su buƙaci isa zagayen daf da na kusa da na karshe (Quarterfinals) wanda ke nufin ƙungiyoyi biyu suna buƙatar lashe zagaye na 16 da zagaye na 32.
Hakan zai iya haifar da fafatawa tsakanin zakarun biyu a zagayen wasan daf da na kusa da na karshe na ƙungiyoyi takwas (Quarterfinals).


