Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe ta gabatar da cakunan inshorar rayuwa da inshorar hatsari na ƙungiya, waɗanda jimillar kuɗinsu ta kai naira miliyan 14.55, ga iyalai 21 na ’yan sandan da suka rasu ko suka samu raunuka.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe ya rabawa manema labarai, an bayyana cewa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Umar Ahmed Chuso, ne ya gabatar da cakunan a hedikwatar rundunar da ke Gombe, a wani mataki na tallafa wa jami’an ’yan sanda da iyalansu.
Jimillar kuɗin da aka gabatar ya kai ₦14,550,092.10, wanda aka tanada domin ba da tallafin kuɗi ga waɗanda suka cancanta, waɗanda ’yan uwansu suka rasu ko suka samu raunuka yayin gudanar da ayyukan hidimar ƙasa.
Yayin gabatar da cakunan, CP Chuso ya jajantawa iyalan jami’an da suka rasu, tare da yaba musu bisa jajircewa, juriyar da suka nuna da kuma irin sadaukarwar da suka yi.
Kwamishinan ya kuma buƙaci waɗanda suka amfana da kuɗaɗen da su yi amfani da su yadda ya kamata, yana mai jaddada cewa jin daɗin jami’an ’yan sanda da iyalansu, da kuma iyalan jami’an da suka rasu, na daga cikin muhimman abubuwan da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ke bai wa muhimmanci.
Ya ce inganta jin daɗin jami’an ’yan sanda na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ingantaccen aikin tsaro, tare da sake tabbatar da ƙudirin rundunar na ci gaba da tallafa wa jami’anta da iyalansu.
A nasu ɓangaren, waɗanda suka amfana da tallafin sun nuna godiyarsu ga Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, da kuma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, bisa wannan karamci da kuma tunawa da irin sadaukarwar da ’yan uwansu suka yi wajen yi wa ƙasa hidima.
Gabatar da cakunan na daga cikin matakan da Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya ke ɗauka domin inganta jin daɗin jami’an ’yan sanda da iyalansu, da kuma kula da iyalan jami’an da suka rasu.


