Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Shugaba Bola Tinubu Ya Amince Da Inganta Wutan Lantarki A Kasar
Published: April 6, 2026 at 10:52 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya amince da shirin biyan bashin naira tiriliyan 3.3 domin warware tsofaffin basussukan da suka daɗe suna addabar ɓangaren wutar lantarki a Najeriya.

Sanarwar daga fadar shugaban ƙasar ta ce bashin ya taru ne daga shekarar 2015 zuwa 2025, kuma an cimma yarjejeniya kan adadin domin kawo ƙarshen matsalar cikin gaskiya.

A sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar ya ce, an riga an fara aiwatar da shirin, inda kamfanonin samar da wuta 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar biyan naira tiriliyan 2.3, yayin da gwamnati ta tara naira biliyan 501, ciki har da biliyan 223 da aka riga aka biya.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu Arowolo-Verheijen, ta ce shirin zai taimaka wajen daidaita harkar wuta, ƙara amincewa, da inganta samar da lantarki.

Ta ƙara da cewa gyare-gyaren sun haɗa da inganta mitoci da kuma farashin da ya dace da ingancin wuta, tare da ba da fifiko ga kasuwanci da masana’antu.

Tinubu ya yaba da gudunmawar masu ruwa da tsaki, yana mai cewa za a fara mataki na gaba na shirin nan ba da jimawa ba.

Afrika, Labarai, Najeriya, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: Sojojin Amurka Sun Kutsa Cikin Kasar Iran
Next Post: Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi A Edo

Karin Labarai Masu Alaka

An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe Labarai
Kamfanin Mai Mallakar Saudiya Aramco Zai Sanja Hanyar Fitar Da Danyen Mai Labarai
Farashin Kasuwar Yawon Bude Ido A Kasuwar Hannayen Jari Ya Fadi Afrika
Farashin Mai Ya Cigaba Da Tashi Afrika
Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Roger Lumbala Shekaru 30 Labarai
Ba Mamaki APC Ta Kafa Tarihi A Ranar Litinin Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jami’an Tsaro A Jihar Borno Sun Kama ‘Yan Bindiga
  • Farashin Mai Ya Cigaba Da Tashi
  • Shugaba Trump Yayi Barazanar Tarwatsa Cibiyar Makamashin Iran
  • Matatar Man Dangote Ta Kara Yawan Mai Dake Zuwa Kasashen Afirka
  • Kungiyar Kiristoci Ta Karyata Kubutar Da Mambobin Su A Kaduna

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi A Edo Afrika
  • Kasar Chadi Ta Rufe Iyakar Ta Da Kasar Sudan Afrika
  • Amurka Tace Zata Gama Yakin Iran Cikin Makonni Afrika
  • Shugaba Trump Yayi Barazanar Tura Sojoji Ga Masu Zanga Zanga Amurka
  • NUJ: Akwai Bukatar Samar Da Inshorar Lafiya Ga ‘Yan Jarida A Najeriya Rediyo
  • Sunayen Jakadu: Kungiyar CISLAC Ta Nemi A Janye Sunan Mr. Ayodele Oke Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Iran Zata Sassauta Shirin Nukiliya Tsakaninta Da Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.