Mashawarcin shugaban kasar kan harkokin yada labarai da tsare tsare, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Gwamnonin sun kunshi na Sakkwato Ahmad Aliyu, Ondo, Lucky Aiyedatiwa, sai Gwamnan Jigawa Umar Namadi.
Sauran sune Gwamnan Kebbi, Dakta Nasir Idris, Kogi, Ahmed Usman Ododo da kuma Gwamnan Edo, Monday Okpebholo.
Tattaunawar ta Shugaban Kasar da Gwamnonin ta dai kare ba tare da jawabin ga manema labarai ba, akan me aka tattauna.


