Shugaba Tinubu ya mika sunayen Sabbin Shugabannin NMDPRA da NUPRC bayan murabus din Farouk Ahmad da Gbenga Komolafe

Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen mutane biyu domin tantancewa da amincewa a matsayin sababbin shugabannin hukumomin kula da harkokin mai da iskar gas na ƙasa.
Nadin ya biyo bayan murabus ɗin Injiniya Farouk Ahmed daga Hukumar Kula da Bangaren Mai da Gas na ƙasa (NMDPRA), da kuma Gbenga Komolafe daga Hukumar Kula da Hakar Mai ta Ƙasa (NUPRC).
An naɗa tsoffin Shugabannin ne a shekarar 2021 a zamanin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, bayan kafa hukumomin ƙarƙashin Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA).
A wasiƙar da ya aike wa Majalisar Dattawa, Shugaba Tinubu ya nemi a gaggauta tantancewa da amincewa da Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan a matsayin Babbar Darakta-Janar (CEO) ta NUPRC, da kuma Injiniya Saidu Aliyu Mohammed a matsayin Babban Darakta-Janar (CEO) na NMDPRA.
Eyesan ta kammala karatun Tattalin Arziki a Jami’ar Benin, kuma ta shafe kusan shekaru 33 tana aiki a Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) da rassa sannan ta yi ritaya a matsayin Mataimakiyar Shugabar Sashen Upstream (2023–2024), sannan ta rike mukamin Babbar Manaja ta Tsare-tsare da Dabaru daga 2019 zuwa 2023.
A nasa bangaren, Injiniya Saidu Aliyu Mohammed, haifaffen jihar Gombe a 1957, ya kammala digiri a fannin Injiniyan Sinadarai a Jami’ar Ahmadu Bello a 1981 kuma kwanan nan an sanar da shi a matsayin Darakta mai zaman kansa a kamfanin Seplat Energy.
Ya taba rike mukaman Darakta-Janar na Matatar Mai ta Kaduna da Kamfanin Iskar Gas na Najeriya, tare da shugabancin kwamitocin gudanarwa na West African Gas Pipeline Company.
Haka kuma, ya taba zama Darakta-Janar kuma Mataimakin Shugaban Ayyuka (COO) na Sashen Gas da Wutar Lantarki, inda ya taka rawa a manyan tsare-tsaren gas na ƙasa, ciki har da Gas Masterplan, Gas Network Code, da kuma bayar da gudummawa wajen tsara dokar PIA.

Injiniya Saidu Mohammed ya kasance cikin masu jagorantar manyan ayyuka kamar fadada bututun iskar gas na Escravos–Lagos, aikin bututun Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), da ayyukan Nigeria LNG.


