Shugaba Tinubu ya nada Amb Isma’il Abba Yusuf a matsayin sabon shugaban hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya nada Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaba hukumar kula da aikin hajji ta kasa, NAHCON. Nada shi na bukatar amincewar Majalisar Dattawa kamar yadda dokar NAHCON ta 2006 ta tanada.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan Yada Labarai, Mr Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Bola Tinubu ya aika wasika ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, yana neman majalisar ta tabbatar da nadin cikin gaggawa. Ambasada Ismail Abba Yusuf zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman wanda ya yi murabus a wannan mako bayan shafe kusan watanni 14 a mukamin.
Sanarwar ta bayyana cewa Ambasada Ismail Abba Yusuf gogaggen jami’in diflomasiyya ne, wanda ya taba zama jakadan Nijeriya a kasar Türkiye daga 2021 zuwa 2024. Ana sa ran nadin nasa zai taimaka wajen ci gaba da tafiyar da harkokin aikin Hajji da ayyukan NAHCON.


